Posts

Showing posts from February, 2020
Tarihin Daura kafin zuwan bayajidda  Amma zan ɗan takaita saboda yanayi na rubutu! Abduddar ɗa ne ga Najibu. Asalin mutanen kasar kan'ana ne kuma rashin samun sarauta ne ya baro su daga garin su a karni na 20 kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam a wani kaulin kuma a karni na 13 shekarar masihiyya. Sun bar kan'ana zuwa Falasɗinu da misra da Tarabulus. Tafiya tafiya har inda samu kansu a wani dausayi inda suka yi zango. Wannan ya jawo sauran makotantan gidajen dake gefe da su suka taho suka haɗe inda suka kafa ainahin tsohon garin Daura. Abduddar ne ya jagoranci mutanen wannan gari kuma bayan da Allah ya yi masa rasuwa, wadda saboda iya tafiyar da jagoranci a gare su, sai mutanen wannan gari suka  mikawa ƴaƴansa jagorancin su. Ƴaƴan sa mata 9 suka mulki mutanen wannan gari wanda a ita ta taran ne mai suna Daura aka sakawa garin suna Daura kuma ake kiran saurautar garin da suna Daurama.  *Jerin sunayen wadannan mata sarauniyoyi guda tara (9) ƴaƴa da jikokin Abduddar...