Tarihin Daura kafin zuwan bayajidda
Amma zan ɗan takaita saboda yanayi na rubutu!
Abduddar ɗa ne ga Najibu. Asalin mutanen kasar kan'ana ne kuma rashin samun sarauta ne ya baro su daga garin su a karni na 20 kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam a wani kaulin kuma a karni na 13 shekarar masihiyya.
Sun bar kan'ana zuwa Falasɗinu da misra da Tarabulus. Tafiya tafiya har inda samu kansu a wani dausayi inda suka yi zango. Wannan ya jawo sauran makotantan gidajen dake gefe da su suka taho suka haɗe inda suka kafa ainahin tsohon garin Daura.
Abduddar ne ya jagoranci mutanen wannan gari kuma bayan da Allah ya yi masa rasuwa, wadda saboda iya tafiyar da jagoranci a gare su, sai mutanen wannan gari suka mikawa ƴaƴansa jagorancin su. Ƴaƴan sa mata 9 suka mulki mutanen wannan gari wanda a ita ta taran ne mai suna Daura aka sakawa garin suna Daura kuma ake kiran saurautar garin da suna Daurama.
*Jerin sunayen wadannan mata sarauniyoyi guda tara (9) ƴaƴa da jikokin Abduddar waɗanda suka mulki Daura sune*
👇🏾👇🏾👇🏾
1 Kufuru
2 Gino
3 Yakumo
4 Yakanya
5 Walzamu
6 Yambamu
7 Gizir-gizir
8 Inna-gari
9 Daura
Sarauniya Daurama taci gaba da sarauta inda wata rana a yawon ta na shakatawa taje wani dausayi inda taga wata rijiya. Ita wannan rijiya ita ake kira da suna Kusugu. Taci gaba da zuwa wannan guri saboda yana bata sha'awa kuma ga wannan daɗaɗɗiyyar rijiya, har inda daga karshe suka tashi daga wancan tsohon guri suka kafa sabon Garin Daura na yanzu inda rijiyar kusugu take. Ga duk wanda yaje garin Daura har yanzu akwai kufan wancan tsohon gari ana cewa da shi tsohon birni. Kuma an kafa signboad a gefen kufan garin inda aka rubuta Tsohon Birni
A Sabon garin da Sarauniya Daura ko Daurama ta kafa wanda yake shine garin Daura na yanzu, an samu karin wasu sarauniyoyi mata har guda 8 daga jikokin Abduddar kafin zuwan bayajidda.
*Ga jerin sunayen su kamar haka:*
👇🏾👇🏾👇🏾
1 Gamata
2 Shata
3 Batatuma
4 Sandamata
5 Jamata
6 Hamata
7 Zama
8 Shawata
Don haka a lokacin Mulkin Sarauniya Shawata ne Abu Yazid ko Bayajidda yazo wannan gari na Daura inda ya sauka a gidan wata tsohuwa da ake kira Ayyana.
Zan tsaya a nan sai kun sake jina watakila a wata gabar!
Wannan tarihi akwai shi a wani littafi na kundin tarihin Daura da ake kiran sa da suna *GIRGAM* !
KABIR ELYAKUB ZAKIRAI

Sunana Kabir Elyakub Zakirai Ni me nazari ne a harshen Hausa kuma dalibi ne Number ta 08036434771
ReplyDelete